Amurka ta rasa mafakarta ta mai kare hakkin bil adama a 2021
2022-03-01 10:20:24 CRI
Sakamakon binciken ra’ayin jama’ar Amurka da aka fitar a kwanakin baya, ya nuna cewa, sama da rabin Amurkawa suna mayar da shekarar 2021 a matsayin shekara mafi wahala, lamarin da ya shaida cewa, yanayin kare hakkin bil adama da Amurka ke ciki ya kara tsananta.
Da farko, gaza dakile yaduwar annobar cutar COVID-19 ya jefa al’ummun kasar ta Amurka cikin mawuyacin hali. A shekarar 2021, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar suka kamu da cutar a Amurka ya kai miliyan 34.51, kuma adadin mutanen da suka rasa rayuka sakamakon cutar ya kai dubu 480, adadin da ya kai sahun gaba a duniya. Ana iya cewa, dalilin hakan shi ne ‘yan siyasar Amurka, sun yi watsi da lafiyar al’ummun kasar, tare da siyasantar da annobar.
Kana sakamakon binciken ya nuna cewa, matasan Amurka kaso 7 bisa dari kacal ne ke ganin cewa, Amurka tana gudanar da tsarin demokuradiya yadda ya kamata.
Hakika a shekarar 2021, Amurka ta rasa mafakarta ta kasancewa mai kare hakkin bil adama, gwamnatin Amurka ta nuna wa al’ummun kasa da kasa yadda take rasa kimar “hakkin bil adama mai salon Amurka” ta hanyar daukar hakikanin matakai. Misali kan hakan akwai tashin hankalin da ya faru a babban ginin majalisar dokokin kasar a watan Janairu, da janyewar sojojin kasar daga Afghanistan a watan Agusta, da gaza samun sakamako yayin taron kolin demokuradiya a watan Disamba.
An lura cewa, ma’anar “hakkin dan adama” a zukatun ‘yan siyasar Amurka ita ce, “nuna fin karfi”. Don haka, kasashen duniya da dama a yayin taro karo na 48 na majalisar kare hakkin bil adama ta MDD da aka kira a shekarar 2021 ke cewa, Amurka kasa ce mai gurgunta sha’anin kare hakkin bil adama na duniya. (Jamila)