Jakadan Sin dake Nijar ya gana da tsohon jakadan Nijar dake Sin
2022-03-01 15:17:38 CRI
Jiya Litinin, jakadan kasar Sin dake Jamhuriyar Nijar, Jiang Feng, ya gana da tsohon jakadan Nijar dake kasar Sin, Inoussa Moustapha, inda suka yi musanyar ra’ayi kan alakokin kasashen biyu.
Jakadan Jiang ya ce, akwai dadadden zumunci tsakanin Sin da Nijar. A ‘yan shekarun nan, bangarorin biyu na kara samun fahimtar juna ta fannin siyasa, kuma hadin-gwiwarsu na samar da alheri ga jama’ar kasashen biyu. Jakada Jiang yana kuma fatan jakada Moustapha zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen sada zumunta tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Shi ma a nasa bangaren, jakada Moustapha ya ce nasarorin da aka samun wajen karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu, na hakika ne. Ya ce Nijar ta godewa kasar Sin bisa goyon-baya, da taimakon da take samar mata a fannin raya tattalin arziki, da kyautata rayuwar al’ummar Nijar. Moustapha ya kara da cewa, babban ci gaban da kasar Sin ta samu tun da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ya burge shi matuka, inda a cewarsa, yana fatan kara azama wajen samar da ci gaba ga alakokin Nijar da Sin. (Murtala Zhang)