logo

HAUSA

Rasha vs Ukraine: Adalci ne kadai zai kashe wutar rikici amma ba daukar bangare ba

2022-02-28 18:52:49 CRI

Tun bayan takaddamar da ta kaure tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, hankulan duniya ya karkata matuka game da abin da ke faruwa dangane da rashin fahimtar da ta kunno kai tsakanin kasashen biyu. Ko da yake, sanin kowa ne ita fitina ba abar so ba ce, kuma duk lokacin da fitina ta taso, abu mafi muhimmanci shi ne a yi kokarin hada hannu tare domin kashe ta don gudun mai zai je ya zo. A wannan yanayin da ake ciki, babban kuskure ne wasu kasashe su dinga bayyana kalamai da ra’ayoyin dake iya kara ruruta wutar rikicin, abu mafi dacewa shi ne su mayar da hankali wajen lalibo hanyoyin daidaita takaddamar kasashen, da tausasa zukatansu domin su yarda su hau kan teburin tattaunawar sulhu don kawo karshen rikicin da kuma yayyafawa rikicin ruwan sanyi. Bugu da kari, batun barazanar da wasu kasashe da kungiyoyi ke yi na sanya takunkumi ba zai haifar da da mai ido ba, kuma ba zai taimaka wajen warware rikicin ba. Har kullum, kasar Sin babban burinta shi ne a yi kokarin dinke duk wata baraka, da warware sabanin fahimta ta hanyar tattaunawar siyasa, alal misali, koda a karshen wannan makon mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta ta wayar tarho da sakatariyar harkokin wajen kasar Birtaniya Liz Truss, da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Josef Borell, da mai ba da shawara ga shugaban kasar Faransa, Emmanuel Bonne, inda suka mai da hankali kan musayar ra'ayoyi game da halin da ake ciki a Ukraine. Game da matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun Ukraine, Wang Yi, ya bayyana wasu fannoni biyar. Na farko, ya ce, kasar Sin tana tsayawa kan mutunta mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa na kasashe daban daban, da kiyaye manufofi, da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD. Wannan shi ne matsayin da take bi a ko da yaushe, wanda kuma ya dace da batun Ukraine. Na biyu, kasar Sin tana ba da shawarar bin ra'ayin tsaro na bai daya, da cikakken hadin kai mai dorewa. A ganinta, bai kamata a tabbatar da tsaron wata kasa ta hanyar tauye tsaron wasu kasashe ba, kuma ba za a iya tabbatar da tsaron yankin ta hanyar karfafa ko fadada kungiyoyin soja ba. Na uku, kasar Sin tana mayar da hankali kan sauyin yanayin da Ukraine ke ciki, halin da kasar ke ciki yanzu wani abu ne da ba a so ganin haka ba. Na hudu, kasar Sin tana goyon baya da karfafa duk wani yunkurin diflomasiyya da zai taimaka wajen warware rikicin Ukraine cikin lumana. Kasar Sin tana maraba da yin shawarwari kai tsaye tsakanin Rasha da Ukraine cikin sauri. Na biyar, kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya taka muhimmiyar rawa wajen warware batun Ukraine. Kuma kamata ya yi matakan da kwamitin zai dauka su kasance na kwantar da hankulla, amma ba na rura wutar rikicin ba. Alamun sun bayyana cewa, shugabannin kasashen Rasha da Ukraine sun bayyana aniyarsu ta shiga tattauanwar sulhu. Koda a karshen wannan mako, an jiyo shugaban kasar Rasha Vladmir Putin, ya bayyana aniyar Rasha na hawan teburin sulhu da bangaren Ukraine, rahotanni na cewa, a karshen mako Rashar ta aike da tawagar wakilanta daga ma’aikatun harkokin waje, da ta tsaro, da sauran hukumomin gwamnati zuwa birnin Gomel na kasar Belarus domin tattaunawa da Ukraine. Koda yake, da farko an bada labarin cewa shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya nuna kin amincewarsa da halartar tattaunawar a kasar Belarus, amma daga bisani, ya zuwa karfe 10 na daren ranar 27 ga watan Fabrairu bisa agogon Beijing, an bada labarin cewa, shugaban kasar Ukraine ya amince da yin shawarwari tare da Rasha a bakin iyakarta da kasar Belarus. Sannan a yau Litinin an labarta cewa, tawagar wakilan Ukraine ta riga ta isa kasar Belarus. Yanzu babban abin da ake fata dai shi ne, a warware wannan rikici da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu, domin a samu wanzuwar zaman lafiya a shiyyar da ma duniya baki daya. (Ahmad Fagam)