Me Kasar Sin Ta Kawo Wa Duniya A Shekarar Da Ta Gabata?
2022-02-28 20:38:31 CRI
Yau Litinin hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta gabatar da rahoton kididdiga kan ci gaban kasar Sin a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa a shekarar 2021.
Rahoton ya cewa, duk da kalubaloli da dama da ake fuskanta a ciki da wajen kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, amma kasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki da kaso 8.1 cikin dari, kana yawan karuwar GDP na ko wane mutum ya kai kaso 8 cikin dari. Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya kara babban kuzari kan tattalin arzikin duniya, wanda ake kokarin farfado da shi.
Ban da haka kuma, tattalin arzikin kasar Sin yana mara wa tattalin arzikin duniya baya sosai. A shekarar 2021, gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ta kai kaso 25 cikin dari. Jimilar kudaden shigi da ficin kayayyaki ta kai kudin Sin Yuan triliyan 39.1 a kasar Sin, wanda ya karu da kaso 21.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2020, don haka kasar Sin ta shafe shekaru 5 a jere tana zama ta farko a duniya a fannin cinikin kayayyaki. Hakan ya nuna cewa, kasashen duniya na bukatar kayayyaki kirar kasar Sin. Al’ummar kasar Sin na sayen kayayyaki daga sassa daban daban duniya, abin da ke nuna karin bukatunsu.
Har ila yau, kasuwar kasar Sin ta kara samar wa kamfanonin kasa da kasa damar samun ci gaba. A shekarar 2021, yawan sabbin kamfanoni masu jarin waje ya kai dubu 61 a kasar Sin, wanda ya karu da kaso 23.3 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2020.
Duk da rashin tabbas da ake fuskanta a duniya, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da kara ba da tabbaci kan farfado da tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)