logo

HAUSA

Gwamnatin Xinjiang ta yi Allah wadai da dokar Amurka ta“Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”

2021-12-25 16:59:20 CRI

Gwamnatin Xinjiang ta yi Allah wadai da dokar Amurka ta“Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”_fororder_新疆社区

Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, a ranar Juma’a ta yi Allah wadai da matakin kasar Amurka na amincewa da dokar da ta kira “haramta tilastawa al’ummar Uygur kwadago”.

A shekarun baya-bayan nan, Xinjiang ta ba da fifiko kan samar da ayyukan yi da nufin inganta zaman rayuwar al’ummar jihar, kuma ta samu cikakkiyar nasarar samar da ayyukan yi ga wadanda ke da damar yin ayyuka a jihar, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, yawan mutanen da suka samu ayyukan yi a Xinjiang ya karu daga mutane kusan miliyan 11.35 a shekarar 2014 zuwa mutane miliyan 13.56 a shekarar 2020, adadin da ya karu da kashi 19.4 bisa 100.

Yayin da take kokarin daga matsayin samar da ayyukan yi, jihar Xinjiang tana kuma kokarin kiyaye hakkoki da moriyar al’umma bisa doka. Babu wani batun da ake kira da suna wai “aikin tilas " a jihar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Batun Xinjiang wata harka ce dake shafar al’amurran cikin gidan kasar Sin, don haka babu wanda ke da ikon yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Sin, inji sanarwar.(Ahmad)

Ahmad