Yunkurin Amurka Na Dakile Ci Gaban Kasar Sin Bisa Hujjar Xinjiang Ba Zai Yi Nasara Ba
2021-12-22 21:24:08 CRI
Kwanan baya, kasar Sin ta sanar da daukar matakin ramuwa kan kasar Amurka, bisa dokarta ta kin yarda da takunkumin kasashen waje, wato kasar Sin ta sanya takunkumi kan jami’ai 4 na kwamitin kasa da kasa na Amurka mai kula da ‘yancin addinai, kamar yadda Amurka ta kakaba wa jami’an Sin 4, bisa hujjar hakkin dan Adam mai nasaba da jihar Xinjiang.
Dalilan da suka sa kasar Sin ta yi hakan su ne, kare ikon mulkin kanta, da moriyarta ta fuskar tsaro da bunkasuwa, da kiyaye ka’idojin rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida, da yin adalci a fannin ikon mulkin kasa, lamarin da ya nuna aniyarta ta kin yarda da danniya da siyasar fin karfi.
Amurka ta kakaba wa jami’an kasar Sin takunkumi ne bisa karya da labarun bogi. Kasar Sin ta dade tana yin karin bayani kan wajibcin daukar matakan yaki da ta’addanci a jihar Xinjiang, da ainihin dalilan da suka sa Xinjiang ta samu wadata da ci gaba. Amma ‘yan siyasar Amurka sun rufe kunnensu, sun shafa wa kasar Sin bakin fenti, a yunkurin hana ci gaban Xinjiang, da ma bunkasuwar kasar Sin.
Mutanen 4 da kasar Sin ta sanar da kakabawa takunkumi, jami’ai ne na kwamitin kasa da kasa na Amurka mai kula da ‘yancin addinai, wanda ya dade yana kallon kasar Sin bisa tunaninsa na siyasa, tare da fito da rahoton shekara-shekara sau da dama, kan manufofin kasar Sin game da addinai, da halin da Sin take ciki ta fannin addinai, a yunkurin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Don haka kasar Sin ta sanar da sanyawa wadannan mutane 4 takunkumi mai karfi.
Har kullum, kasar Sin ba ta yarda da kasashen waje su tsoma baki cikin batun Xinjiang. Kuma yunkurinsu na dakile ci gaban Xinjiang ba zai yi nasara ba. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Neman Ci Gaban Bai Daya Abu Ne Da Ya Dace Sin Da Amurka Su Maida Hankali A Kai
- Zhao Lijian: Amurka ce kan gaba wajen yiwa kasashen duniya matsin lambar tattalin arziki
- Sin ta dauki matakin ramuwa bisa takunkumin Amurka
- Sin Na Maraba Da ‘Yan Wasa Daga Dukkanin Sassan Duniya Zuwa Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing