logo

HAUSA

An fara kada kuri’u a zaben ‘yan majalissar wakilan Somalia

2021-11-02 10:50:56 CMG

An fara kada kuri’u a zaben ‘yan majalissar wakilan Somalia_fororder_1102-saminu-3

A jiya Litinin ne al’ummun kasar Somalia, suka fara kada kuri’u a zaben ‘yan majalissar wakilan kasar da aka jima ana dako, inda aka fara da zaben ‘yan majalissar Somaliland su 2 a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar. ‘Yan takara 4 ne dai ke neman kujerun majalissar 2, ciki har da mataimakin firaministan kasar Mahdi Mohamed Guled.

Za a zabi wakilan jam’iyyu ne bisa tsarin hadin gwiwa da kungiyoyin fararen hula, da shugabannin al’umma, da kuma wakilan gwamnatin jihohi. An kuma tsara gudanar da zaben a wurare 2 a duk jiha, maimakon wurare 4 da a baya ake kada kuri’un.

Firaministan kasar Mohamed Hussein Roble, ya taya sabbin zababbun ‘yan majalissar 2 daga Somaliland, murnar shiga majalissar wakilan kasar, yana mai kira ga sauran jihohin shiyyoyin kasar da su hanzarta kammala na su zabukan.  (Saminu)

Saminu