logo

HAUSA

Mutane miliyan 2.3 ne ke fama da karancin ruwa da abinci a Somalia

2021-11-20 15:44:14 CMG

Mutane miliyan 2.3 ne ke fama da karancin ruwa da abinci a Somalia_fororder_1120-somalia-Faeza

MDD ta ce mutane kimanin miliyan 2.3 a Somalia, ko kaso 18 na al’ummar kasar, na fama da matsanancin karancin ruwa da abinci da abincin dabbobi.

Stephane Dujarric, kakakin sakatare janar na MDD, ya bayyana yayin taron maneman labarai na jiya cewa, gwamnatin Somalia da kungiyoyin agajin jin kai, sun ce sun kadu da yadda matsalar fari ke kara ta’azzara a kasar.

Ya ce ana fuskantar barazanar karuwar cututtukan dake yaduwa ta ruwa, saboda rashin ruwa mai tsafta.

Ya kara da cewa, Somalia na kan gaba a fannin fuskantar tasirin sauyin yanayi. Kuma tun daga shekarar 1990, ta fuskanci matsalolin da suka shafi yanayi sama da 30, ciki har da fari 12 da ambaliyar ruwa 19.

Kusan mutane 100,000 ne suka bar gidajensu, musammam a yankunan tsakiya da kudancin kasar domin neman abinci da ruwa da abincin ga dabbobinsu. Kuma sama da kaso 70 na al’ummar kasar na rayuwa ne kasa da mizanin talauci. (Fa’iza Mustapha)

Faeza