logo

HAUSA

Sin ta sha alwashin tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya a Somalia

2021-08-13 11:26:54 CMG

Sin ta sha alwashin tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya a Somalia_fororder_2

Mukaddashin babban jagoran tawagar dindindin ta kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce kasar sa a shirye take ta tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Somalia.

Dai Bing wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Alhamis, yayin zaman kwamitin tsaron majalissar da aka gudanar, game da yanayin da ake ciki a Somalia, ya ce Sin ta sha alwashin yin aiki tare da sassan kasa da kasa, wajen tabbatar da yanayi na lumana da ci gaba a Somalia.

Ya ce "A baya bayan nan, yanayin siyasar kasar ya fara kyautata. Kuma Sin ta yi maraba da yarjejeniyar da sassan siyasar Somalia suka cimma, game da shirin gudanar da zabukan kasar, da kuma kaddamar ayyukan majalissar dattijan kasar. Kaza lika Sin za ta ci gaba da taimakawa rundunar AMISOM, a ayyukan ta na tsare tsare, da hadin gwiwa da jami’an tsaron Somalia, domin cimma nasarar ayyukan yaki da ta’adanci. Har ila yau Sin na fatan kasashen duniya za su tallafawa gwamnatin Somalia, wajen raya sanin makamar aiki, daidai da bukatun kasar na mika mulki bisa managarcin tsari.  (Saminu)

Saminu