Majalissar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”
2021-12-24 20:29:25 CRI
Kwamitin dake lura da harkokin waje, na majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, ya yi Allah wadai da dokar da Amurka ta kafa, mai lakabin “haramta tilastawa al’ummar Uygur kwadago”.
Wata sanarwar da kwamitin ya fitar a Juma’ar nan, ta bayyana dokar da Amurka ta kafa, a matsayin matakin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, ta hanyar fakewa da ‘yancin bil Adama.
Kaza lika sanarwar ta ja kunnen Amurka da cewa, muddin ta nacewa bin wannan mummunar hanya, ba shakka Sin za ta mayar da martani mai karfi da ya dace. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba
- Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”
- Amurka Wadda Ta Kashe Wadanda Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba Ba Ta Da Matsayin Zargin Wasu Kan Hakkin Dan Adam
- Zhao Lijian: Gwamnatin Amurka ta yi watsi da aikin kare rayukan al’ummun ta da ma na sauran al’ummun duniya
- Yunkurin Amurka Na Dakile Ci Gaban Kasar Sin Bisa Hujjar Xinjiang Ba Zai Yi Nasara Ba