logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka kamu da nau’in Omicron a Najeriya ya kai 51

2021-12-25 16:47:57 CRI

Yawan mutanen da suka kamu da nau’in Omicron a Najeriya ya kai 51_fororder_omicron2

Hukumomin lafiyar tarayyar Najeriya sun sanar a ranar Juma’a cewa, an sake gano karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ta nau’in Omicron, inda adadin sabbin masu kamuwa da cutar ta Omicron ya kai 51 a kasar baki daya.

Ifedayo Adetifa, shugaban hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar Najeriya (NCDC), ya fada wa manema labarai a wani taron manema labaru a Abuja, babban birnin kasar cewa, a cikin wadanda suka kamu da cutar ta nau’in Omicron a kwanan nan, babu wanda ya yi tafiye-tafiye a kwanan baya, sai dai da ma yana cikin kasar, wanda hakan ya nuna cewa, kasar ta jima tana fama da yaduwa nau’in cutar a tsakanin al’umma.

Jami’in hukumar ta NCDC ya jaddada cewa, ya dace ‘yan Najeriya su dinga kiyaye dokar ba da tazara tsakanin juna kuma su guji yin mu’amala da mutanen da suka nuna alamomin kamuwa da cutar sarkewar numfashi.

Ya kuma shawarci al’ummar kasar Najeriya da su kara daukar matakan dakile yaduwar cutar nau’in Omicron, ta hanyar takaita gangamin jama’a, da tabbatar da ba da tazara a tsakanin juna, kana da rage yawan cudanya, kuma a gaggauta rufe wuraren da ake fargabar akwai barazanar yaduwar nau’in cutar.(Ahmad)

Ahmad