Najeriya ta ce sojojinta sun kashe mayakan IS da dama
2021-11-29 20:15:18 CRI
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan kungiyar IS ta yammacin Afirka (ISWAP) da dama, yayin da suka kai hari a wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Wata sanaewa da Onyema Nwachukwu ya fitar na cewa, sojoji biyu ne suka mutu sakamakon harin da kungiyar ISWAP ta kai a ranar Lahadi a sansanin sojojin da ke karamar hukumar Gajiram Nganzai a jihar Borno.
Ya bayyana cewa, ayarin jiragen sama na Operation Hadin Kai, dake daukar matakan soja a yankin arewa maso gabashin kasar, ya yi barin wuta kan ‘yan ta’addan da suka yi yunkurin kutsawa cikin sansanin. (Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Najeriya ta janye dakatarwar da ta yiwa kamfanin jiragen saman Emirates
- Masanin Najeriya: Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Wadatar Da Kowa A Kasar Ya Cancanci Kasashe Masu Tasowa Su Koya
- Najeriya ta doke Liberia inda take dab da yin nasara a share fagen shigar gasar cin kofin duniya
- Ana fargabar gini ya danne mutane 21 a Lagos