logo

HAUSA

Adadin wadanda ‘yan bindiga suka hallaka a Kaduna sun kai mutum 38

2021-12-20 20:26:56 CRI

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, ta ce adadin wadanda suka rasu sakamakon harin ‘yan bindiga a wasu kauyuka 3 a karamar hukumar Giwa sun karu zuwa mutum 38.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce maharan sun aukawa kauyuka 3 da daren Asabar, da kuma safiyar Lahadi.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin na Kaduna, yana mai bayyana lamarin da mummunar ta’asa da ta yi matukar tayar masa da hankali. Shugaba Buhari ya kuma jaddada umarnin da ya baiwa dakarun tsaro, da shugabannin hukumomin leken asiri, na su yi dukkanin mai yiwuwa wajen kakkabe gyauron ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.   (Saminu)

Saminu