Sin ta dauki matakin ramuwa bisa takunkumin Amurka
2021-12-21 20:37:43 CRI
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ta fara aiwatar da wasu matakai na ramuwar gayya, kan matakin Amurka na kakaba takunkumi mai nasaba da batun jihar Xinjiang.
Zhao Lijian, ya ce sakamakon takunkumin da Amurka ta kakabawa wasu Sinawa, da kamfanonin kasar a ranar 10 ga watan Disambar nan, ita ma Sin ta haramtawa wasu Amurka dake aiki a hukumar kasa da kasa, mai lura da ‘yancin addinai shiga babban yankin Sin, da yankin Hong Kong, da Macao, kana an daskarar da kadarorin su dake cikin kasar Sin. (Saminu)
Labarai Masu Nasaba