logo

HAUSA

Zhao Lijian: Amurka ta cancanci a zarge ta da kisan kiyashi

2021-12-06 21:30:55 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Amurka ce kasar da ta fi dacewa a zarge ta da aikata kisan kiyashi. Zhao wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce akwai tarin laifuka da dama na keta hakkokin bil adama kan al’ummu ‘yan asalin kasar ta Amurka wadanda tarihi ya tabbatar, wadanda ko shakka babu ana iya kallon su a matsayin kisan kiyashi.  (Saminu)