logo

HAUSA

Zhao Lijian:Barazanar kauracewa gasar Olympic dake tafe kurari ne kawai na wasu kasashe

2021-12-06 20:23:33 CRI

Zhao Lijian:Barazanar kauracewa gasar Olympic dake tafe kurari ne kawai na wasu kasashe_fororder_赵立坚-2

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce barazanar da wasu ‘yan siyasar kasashen Amurka, da Australia da wasu kasashen yamma ke yi, ta kauracewa gasar Olympic ta lokacin hunturu dake tafe a birnin Beijing, kurari ne kawai maras dalili.

Zhao wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya ce gasar Olympic dake tafe, babbar gasa ce ta kasa da kasa, wadda za ta hallara ‘yan wasa da masu sha’awar wasannin kankara, ba wai wani taro ne da zai baiwa ‘yan siyasar wasu daidaikun kasashe damar yin kurari ba. Don haka a cewar jami’in, barazanar da ‘yan siyasar wadannan kasashe ke yi ba ta da tushe ko makama.  (Saminu)