logo

HAUSA

Zhao Lijian: Wane hurumi Amurka ke da shi na kiran taron dimokaradiyya?

2021-12-07 21:22:07 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce abun mamaki ne ganin yadda kasa kamar Amurka dake yiwa dimokaradiyya karan tsaye, a ce ta kira taron kare dimokaradiyya.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga ikirarin da Amurka ta yi, cewa za ta gudanar da taron ne a matsayin wani mataki na baiwa dimokaradiyya kariya.

Da yake tsokaci game da wasu karairayi da kafar BBC ta kitsa game da Sin, Zhao Lijian ya ce tuni Sinawa ke kallon kafar BBC a matsayin mai nuna banbanci, kuma kafar da ta shahara wajen kirkirar karairayi kan kasar Sin.  (Saminu)