logo

HAUSA

Taron kolin shugabannin Turkiyya da Afrika karo na uku zai bunkasa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban

2021-12-19 16:28:41 CRI

Taron kolin shugabannin kasashen Turkiyya da Afrika wanda ya gudana a ranar Asabar ya cimma matsayar bunkasa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, wanda ya kumshi samar da zaman lafiya da tsaro, da kuma inganta zuba jari kan ababen more rayuwa a Afrika.

A yayin taron kolin hadin gwiwar na Turkiyya da Afrika karo na uku wanda aka kammala a Istanbul, an zartas da wani shirin ayyuka na nan da shekaru 5 masu zuwa.

A jawabin da ya gabatar a taron manema labarai bayan kammala taron, shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce za a goyi bayan  dukkan kokarin bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afrika, kana za a ci gaba da karfafa gwiwar kamfanonin kasar don yin kasuwanci da nahiyar.

Shugaban ya kara da cewa, kasar Turkiyya a shirye take ta tallafawa kasashen Afrika a kokarinsu na yaki da ayyukan ta’addanci, da muggan laifuffuka, da kuma zurfafa hadin gwiwa don yaki da fatara a nahiyar.

Da yake gabatar da jawabin a taron kolin, shugaban kungiyar tarayyar Afrika, kana shugaban kasar Kongo (Kinshasa), Felix Tshisekedi ya ce Afrika tana bukatar muhimman ayyuka, galibi a fannin kasuwanci, ababen more rayuwa, bunkasa aikin gona, shugabanci na gari da kuma kiwon lafiya.

Sama da ministoci 100 da shugabanni 16 na kasashen Afrika ne suka halarci taron kolin na kwanaki uku.(Ahmad)

Ahmad