logo

HAUSA

Turkiyya ta yi Allah wadai da Amurka kan amincewarta game da batun yiwa Armeniyawa kisan kiyashi

2021-04-25 15:41:09 CRI

A jiya Asabar, kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya yi na cewa Amurkar ta yarda mummunan kisan da aka yi wa ‘yan kasar Armeniya a matsayin kisan kare dangi, sama da shekaru 100 da suka shude, ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ne ta bayyana hakan a wata rubutacciyar sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, Turkiyya ta yi Allah wadai da kakkausar murya tare da yin watsi da kalaman da shugaban kasar Amurka ya yi game da batun da ya faru a shekarar 1915, a cewar ma’aikatar, sanarwar ta bayyana cewa babu wasu kwararan shaidu daga masana ko hujjojin da suka dace da shara’a dake nuna goyon bayan ikirarin da shugaban ya yi.

Sanarwar ta ce, kalaman da mista Biden ya ayyana zai yi matukar fama rauni wanda hakan ka iya lalata kyakkyawar dangantaka da aminantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyyar ta kuma bukaci shugaban kasar Amurkan da ya gaggauta gyara wannan babban kuskure, wanda babu abin da zai haifar sai biyan bukatun siyasa.(Ahmad)

Ahmad Fagam