logo

HAUSA

Najeriya da Turkiyya sun kulla yarjejeniyoyi 8 yayin ganawar shugabannin kasashen

2021-10-21 09:37:04 CRI

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Laraba sun kulla manyan yarjejeniyoyi takwas a fannonin makamashi, da masana’antun tsaron kasa, da ma’adanai, a lokacin ganawar shugabannin kasashen biyu a Abuja, babban birnin Najeriya.

Erdogan ya isa Najeriyar ne tun a ranar Talata, a ziyarar aikin kwanaki biyu a kasar, inda nan ne zangon karshe na ziyararsa a kasashen Afrika, gabanin hakan ya ziyarci kasashen Angola da Togo.

Buhari ya bayyanawa taron manema labarai cewa, a lokacin ziyarar Erdogan a kasar mafi yawan al’umma a Afrika, shugabannin biyu sun gudanar da muhimmiyar tattaunawa game da batutuwan dake shafar huldar kasashen biyu, da nufin karfafa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriyar ta Turkiyya.

A cewar shugaban Najeriyar, batutuwan da suka tabo sun hada da fannoni masu yawa wadanda suka kulla yarjejeniya kansu da kuma yarjejeniyar fahimtar juna, wacce suka daddale.(Ahmad)