logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Halarci Bikin Bude Taron Ministocin FOCAC Karo Na 8

2021-11-29 21:27:18 CRI

Da yammacin yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron ministocin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) karo na 8 ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya yi nuni da cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 65 da kafa huldar diflomasiya tsakanin Sin da Afirka. Kasashen Sin da Afirka sun hau kan wata hanya ta musamman ta hadin gwiwa a fannin raya kasa da sake farfadowa. Sun kuma rubuta wani babi mai ban sha'awa na taimakon juna a yayin da ake tsaka da fuskantar sauye-sauye masu sarkakiya, inda suka kafa misali mai haske don gina sabon nau'in alakar kasa da kasa.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ruhin abokantaka da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wani lamari ne da ke nuni da kyakkyawar makoma da akasin haka da ke tsakanin Sin da Afirka, kuma tushen karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. Ya ce, kasar Sin ba za ta taba mantawa da zumunci mai zurfi na kasashen Afirka ba.

Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan gina al'ummomin Sin da Afirka mai makoma ta bai daya a sabon zamani. Na farko, yin aiki tare don yakar annobar COVID-19. Tabbatar da samun allurar rigakafi kuma cikin sauki da araha a Afirka. Na biyu, zurfafa hadin kai a aikace. Ya kamata mu fadada kasuwanci da saka jari, mu raba kwarewa wajen rage talauci da karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki na zamani. Na uku, inganta ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Kasar Sin za ta ba da shawara kan yadda za a samu bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba da rage fitar da iskar carbon, da habaka makamashin da ake iya sabuntawa, da kara karfinmu na samun ci gaba mai dorewa. Na hudu, tabbatar da adalci da daidaito. Kamata ya yi mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da shawarwarin kasashe masu tasowa bisa adalci tare da aiwatar da buri da muradunmu a zahirance na bai daya.(Ibrahim)

Ibrahim