logo

HAUSA

Manufar “Jama’a ne ke jagorantar kasa” ita ce demokradiyya ta ainihi

2021-11-13 20:44:17 CRI

Manufar “Jama’a ne ke jagorantar kasa” ita ce demokradiyya ta ainihi_fororder_微信图片_20211113172042

Sanarwar bayan taro na 6 na kwamitin tsakiya karo na 19 na JKS, da aka fitar a baya-bayan nan, ta takaita dabarun kasar Sin na gina demokradiyya, inda ta jaddada raya demokradiyya dake bada muhimmanci ga jama’a da kuma tabbatar da su ne a gaban komai a kasa. Wannan ya fito da ainihin ma’anar demokradiyya, tare da ba kasashen waje damar tunani da duba mai zurfi, kan irin tsarin demokradiyyar kasar Sin.

Tun bayan kafuwarta, JKS take amfani da kyawawan nasarorin da kasar ta samu daga wayewarta a fannin siyasa da na sauran sassan duniya, inda ta nace kan sanya jama’a gaba da komai a kasar. Tun daga shekarar 2012, JKS ta bunkasa tsarinta na demokradiyya ta kuma kama turbar bayar da muhimminaci ga demokradiyyar dake mayar da hankali kan jama’a. A kasar Sin, zancen “jama’a ne ke jagorantar kasa” ba zance ne na fatar baki ba, muhimmin batu ne da ake gani a zahiri.

Ko kasa tana bin demokradiyya ko a’a, al’ummarta ne ya kamata su bada amsa. Bisa wani nazari na Amurka, kaso 95 na al’ummar Sinawa sun gamsu da shugabancin jam’iyyar, kana kaso 98 sun gamsu da gwamnati. Wannan ita ce amsa mafi gamsarwa da Sinawa ke da shi game da ‘yancinsu na demokradiyya.

Cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta jagoranci jama’a kan tafarkin tsarin demokradiyya dake mayar da hankali kansu. Wannan tafarki ya saba da irin tsarin demokradiyyar yammacin duniya, ya kuma nuna irin kwarin gwiwar da Sinawa ke da shi kan irin nasu tsarin siyasa da zama misali mai ma’ana ga kasashe masu tasowa, wajen lalubar irin tsarin da ya dace da yanayinsu. Karkashinn JKS, Sinawa za su ci gaba da bin tsarin demokradiyyar dake sanya su a gaba da komai.