logo

HAUSA

Xi Ya Yaba Da Kaurar Da Jama’a Daga Inda Rawayen Kogin Ya Yi Ambaliya

2021-10-22 15:50:38 cri

Xi Ya Yaba Da Kaurar Da Jama’a Daga Inda Rawayen Kogin Ya Yi Ambaliya_fororder_8435e5dde71190efdfd1bc97b68ad31ffcfa60ee

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS, Xi Jinping, ya ce kaurar da jama’a daga inda Rawayen Kogi ya yi ambaliya, abun ne da ya yi matukar dacewa.

Xi ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci birnin Dongying na lardin Shandong na gabashin Sin, wato inda aka tsugunar da mutanen.

An gina sabon matsugunin ne ta yadda zai inganta rayuwar mutane daga kauyuka 11 dake kewayen bakin Rawayen Kogi.

Ya kara da cewa, ya yi farin cikin ganin cewa mutanen sun gamsu da yanayin rayuwarsu da kuma aiki, kana suna samun nasarar a kokarinsu na bunkasa yankin.

Ya ce a matsayinta na mai jagora a fannin sarrafa kayayyaki, dole ne Sin ta zama mai dogaro da kanta a fannin makamashi da raya tattalin arziki na ainihi.

Da ya ziyarci rijiyar hakar man fetur ta Shengli dake birnin Dongying, ya karfafawa ma’aikata a wurin gwiwar samar da sabbin nasarori. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)