Sharhi: JKS ba ta da niyyar mulkin danniya tun kafuwarta
2021-11-12 21:55:31 CRI
Jiya ranar 11 ga wata, aka bayar da wata sanarwa a gun cikakken zaman taro na shida na kwamitin tsakiya na karo na 19 na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, inda aka fayyace sirrin jam’iyyar na samun nasarori, wadanda ke jawo hankalin duniya sosai, bisa kalaman dagewa a fannoni goma. A ciki, dagewar kaunar duniya ta kasance daya daga cikinsu, haka kuma ta nuna ra’ayin jam’iyyar wajen daidaita dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.
Yadda JKS ke yin gwagwarmaya a cikin shekaru 100 da suka gabata, ya shaida kalaman babban daraktan kwamitin tsakiya na jam’iyyar Xi Jinping, wato JKS wata jam’iyya ce da ke da burin ganin yadda jama’a suke jin dadin zamansu, kana wata jam’iyya ce da ke gwagwarmaya don ci gaban sha’anin bil Adama.
Tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, ba ta taba ta da yaki da rikici ko sau daya ba. Ba ta taba mallakar yankin sauran kasashe ba. A fannin inganta samun bunkasuwa gaba daya, JKS ta sauke nauyin da ke wuyanta a matsayin jam’iyyar siyasa mafi girma a duniya. A gaban annobar cutar COVID-19 dake addabar duniya, Sin tana samar wa kasashen duniya tallafi gwargwadon karfinta. Yanzu kasar Sin kasa ce da ta fi samar da yawan alluran rigakafi ga waje, kana yawancin alluran rigakafin da kasashe masu tasowa suka samu sun zo daga kasar Sin.
Da duniya ke samun ci gaba yadda ya kamata, da kasar Sin ke yin hakan. Da kasar Sin ke samun bunkasuwa yadda ya kamata, da duniya ke yin hakan. Sinawa har ma daga kwayoyin halittunsu, ba su son kai hari ga saura. JKS ma ba ta da niyyar mulkin danniya a baya, a yanzu da ma a nan gaba.(Kande Gao)