logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Cika Alkawarin Da Ta Yiwa ‘Yan Uwanta Kasashen Afirka

2021-11-30 21:04:55 CRI

Kasar Sin Ta Cika Alkawarin Da Ta Yiwa ‘Yan Uwanta Kasashen Afirka_fororder_afirka

Ranar 29 ga wata, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya sanar da cewa, kasar Sin za ta hada kai da kasashen Afirka wajen gudanar da ayyuka guda 9, mai muhimmanci daga cikinsu, shi ne kiwon lafiya. Kasar Sin ta yi alkawarin samar wa kasashen Afirka karin alluran rigakafin cutar COVID-19 biliyan 1. A cikin wadannan allurai, miliyan 600 daga cikinsu kasar Sin za ta samar da su ne kyauta, miliyan 400 kuma kamfanonin kasar Sin da kasashen Afirka masu ruwa da tsaki ne za su samar da su cikin hadin gwiwa. Wadannan sabbin mataki za su taimaka wajen daidaita matsalar kasashen Afirka ta karancin alluran rigakafin, tare da rage gibin da ake fuskanta a duniya ta fuskar alluran.

Ban da haka kuma, ayyuka guda 9 da shugaban na kasar Sin ya sanar da su, sun shafi rage talauci da ba da gatanci ga manoma, kara azama kan ciniki, zuba jari, yin kirkire-kirkire ta fuskar fasahar zamani, da raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba da dai sauransu, wadanda za su biya bukatun kasashen Afirka a fannonin yaki da annobar, farfado da tattalin arziki da samun ci gaba mai dorewa, sun kuma tsara manufar yin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka cikin shekaru 3 masu zuwa.

Nahiyar Afirka, wuri ne da ya dace kasashen duniya su hada kansu, a maimakon zama wurin yin takara a tsakanin manyan kasashe. A shekarun baya, wasu ‘yan siyasan kasashen yammacin duniya suna kishin dankon zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, har ma suka yi yunkurin lalata alaka dake tsakanin Sin da Afirka. Amma abubuwan da suka yi ba su yi nasara ba.

Yanzu kasar Sin da kasashen Afirka sun samu mafarin gina al'ummomin kasashensu mai makoma ta bai daya a sabon zamani. Kamar yadda ta yi a baya, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi wa ‘yan uwanta kasashen Afirka. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan