logo

HAUSA

FOCAC: Damar Nahiyar Afrika Ta Samun Wadata Da Ci Gaba

2021-11-30 17:17:37 CRI

FOCAC: Damar Nahiyar Afrika Ta Samun Wadata Da Ci Gaba_fororder_FACOC

A jawabinsa da ya yi jiya ga taro karo na 8 na ministocin kasashen dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, shugaban kasar Sin ya gabatar da wasu bangarori da za a kara hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, daga cikinsu akwai aikin gona da yaki da talauci da zuba jari da cinikayya da kirkire-kirkire da sauransu.

Babu yadda za a raba rashin ci gaban kasashen Afrika da talauci, domin shi ne ginshikin galibin matsalolin da kasashen nahiyar ke fuskanta. Kasar Sin ta yi an gani, wato yadda a karshen bara ta kammala fitar da dukkan al’ummarta daga kangin talauci, shekaru 10 kafin lokacin da muradun ci gaba masu dorewa na MDD ya kayyade. Abun nufi shi ne, bayan yabon da kasar Sin ta cancanci samu, lallai ya zama wajibi kasashen duniya su dauki darasi daga wajenta. Bisa la’akari da yadda take a matsayin kasa mai tasowa kamar kasashen Afrika, daukar darasi a wajen kasar Sin ba zai zama wata matsala ba a garesu, kasancewar suna da kamanceceniya a wannan fanni. A ganina, wannan babban bangare ne da ya kamata kasashen Afrika su mayar da hankali kai wajen hada hannu da kasar Sin, musammam bisa duba da cewa ita da kanta ta gabatar da wannan manufa.

Noma aka ce tushen arziki. Galibin kasashen Afrika sun mallaki filaye masu arzikin noma da kuma yawan al’ummar da za su iya ciyar da nahiyar. Yadda Sin ta yi zarra a fannin fasahar zamani har ma da aikin gona, zai zama wata dama ga kasashen Afrika na cin gajiya a wannan fanni. Mayar da hankali kan aikin gona ba ciyar da nahiyar kadai zai yi ba, har ma da zama tushen arzikinta da samar da dimbin ayyukan yi ga jama’a. kana ya kara bunkasa karfin nahiyar na fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje domin kara samun wadata.

Ciniki da zuba jari da kirkire-kirkire. Kasuwar kasar Sin babbar kasuwa ce da duk duniya ke hankoro. Habaka cinikayya da kasar Sin zai kara ba kasashen Afrika damar shiga kasuwar duniya, da kara samun karbuwa. Haka kuma jarinta a kasashensu, zai kara samar musu da ci gaban da suke da muradi. Shaidu sun nuna yadda jarin kasar Sin a kasashen Afrika ya haifar da dimbin ci gaban ababen more rayuwa da kyautatawa tare da saukaka harkokin zamantakewa al’umma. Hakika kara habaka cinikayya da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, zai kara kyautatawa da saukaka rayuwar jama’ar bangarorin biyu. Haka kuma, zai kara fahimtar juna tsakanin al’ummominsu da saukaka muradin da ake da shi na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga bangarorin biyu.(Fa'iza Mustapha)