logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayani game da jawabin Xi Jinping a bikin bude taron ministoci karo na 8 na FOCAC

2021-11-30 20:06:59 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi bayani game da jawabin Xi Jinping a bikin bude taron ministoci karo na 8 na FOCAC_fororder_zhao

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ta kafar bidiyo daga nan birnin Beijing na kasar Sin, tare da ba da jawabi, inda ya waiwayi nasarorin da aka samu a cikin shekaru 65 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da yabawa nasarorin da aka samu daga hadin gwiwar dake tsakaninsu tun bayan taron koli na dandalin FOCAC na Beijing na shekarar 2018, kana Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan yadda za a gina al'ummomin Sin da Afirka mai makoma ta bai daya a sabon zamani wato yin aiki tare don yakar annobar COVID-19, zurfafa hadin kai a aikace, inganta ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tabbatar da adalci da daidaito. Har ila yau Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin za ta hada kai da kasashen Afirka wajen gudanar da ayyuka guda 9, ta fuskar kiwon lafiya, rage talauci da ba da gatanci ga manoma, kara azama kan ciniki, zuba jari, yin kirkire-kirkire ta fuskar fasahar zamani, raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, kyautata kwarewar mulki, yin mu’amalar al’adu da tsaron kasa da shimfida zaman lafiya.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, jawabin Xi Jinping ya nuna shirye-shirye da manufofin da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai mayar da hankali kansu a nan gaba, da tsara taswirar sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a sabon zamani, wanda ya samu yabo daga kasashen Afirka da jama’arsu. Sin za ta aiwatar da ayyuka don cika alkawarin da aka yi a cikin jawabin, da yin kokari tare da kasashen Afirka don aiwatar da ayyukan da shugabannin Sin da Afirka suka cimma a gun taron, da sa kaimi ga raya al'ummomin Sin da Afirka mai makoma ta bai daya a sabon zamani. (Zainab)