logo

HAUSA

Sharhi:Taron FOCAC ya samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka

2021-11-29 21:56:25 CRI

 

 

 

Sharhi:Taron FOCAC ya samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka_fororder_微信图片_20211129212019

A ranar 11 ga watan Yunin bana, an kaddamar da layin dogon tsakanin Lagos-Ibadan dake Najeriya, lamarin da ya faranta ran al’ummar kasar matuka, kuma a yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke gwajin tafiya cikin jirgi a kan layin dogon, ya yi murna da rubuta cewa, “wannan aiki ne da ya kamata mu yaba, kuma muna godiya ga jama’ar kasar Sin da ma gwamnatin kasar.”

Sharhi:Taron FOCAC ya samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka_fororder_微信图片_20211129212004

Kamfanin CCECC na kasar Sin ne ya dauki nauyin gina wannan layin dogon, ta hanyar amfani da fasahohi da na’urori da ma ma’aunin kasar ta Sin.

Babu shakka abin farin ciki ne yadda aka kaddamar da layin dogon, saboda in mun dubi taswirar Nijeriya, za mu ga cewa, kasancewar layin dogon wani muhimmin bangaren na tsarin layukan dogon da gwamnatin kasar ta tsara, wanda baya ga kautata yanayin zirga-zirga a kasar ta Najeriya, ya kuma hada tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Lagos,  wanda hakan ya inganta tsarin sufurin kayayyaki a kasar, tare da aza harsashi mai karfi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Sharhi:Taron FOCAC ya samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka_fororder_9f2f070828381f304ee9186b8025e6006f06f029

Baya ga layin dogon tsakanin Lagos-Ibadan, akwai kuma layin dogo tsakanin Abuja-Kaduna da tashar filin jiragen saman kasa da kasa na Abuja da yankin ciniki marar shinge na Lekki, wadanda dukkansu kasar Sin ce ta gina a Nijeriya. A hakika, karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka(FOCAC), an kaddamar da jerin shirye-shiryen ayyukan more rayuwa, wadanda suka magance matsalolin da ke yi wa ci gaban tattalin arzikin Nijeriya tarnaki, tare da kyautata rayuwar al’ummar kasar.

An kafa dandalin FOCAC ne, a shekarar 2000, wanda ya bude sabon babin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Cikin shekaru 21 da suka wuce, tsarin dandalin ya samar da gaggaruman nasarori ga sassan biyu, abin da har ya sa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ya zama misali na hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Sharhi:Taron FOCAC ya samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka_fororder_1128109863_16381060853071n

Alkaluma sun yi nuni da cewa, tun bayan da aka kafa dandalin, kamfanonin kasar Sin sun gina ko gyara layin dogo sama da kilomita dubu 10 da ma hanyoyin mota kusan kilomita dubu 100 a kasashen Afirka, baya ga kuma gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan dari, tare kuma da samar da guraben aikin yi sama da miliyan 4.5.  Bayan barkewar cutar Covid-19 kuma, kasar Sin ta samar da gudummawar kayayyakin kandagarkin cutar cikin rukunoni 120 ga kasashen Afirka 53 da ma kungiyar AU, tare da samar da alluran rigakafi kusan miliyan 200……

A yau ne aka bude taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal. A daidai lokacin da ake fuskantar manyan sauye-sauye a fadin duniya da ma annobar Covid-19, inda ake fuskantar matsalolin kariyar ciniki da dakushewar tattalin arziki da ciniki, taron na da matukar muhimmanci ga hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ma huldarsu a nan gaba. Ta yaya za su hada kai don fuskantar wadannan kalubalen, da ma sa kaimin farfadowar tattalin arziki da zaman takewar al’umma bayan annobar, Za a samu amsa mai gamsarwa ga wannan tambaya a yayin taron.

Muna fatan taron zai samar da sabon karfin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, ta yadda za a kaddamar da karin shirye-shiryen irinsu layin Dogon Lagos-Ibadan a Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka baki daya, inda ake fatan ganin ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka da kyautatuwar rayuwar al’ummarsu, da ma ci gaban Sin da kasashen Afirka na bai daya.(Lubabatu)