logo

HAUSA

Kuwait ta soke sufurin jiragen sama na kai tsaye zuwa kasashen Afrika 9 sakamakon sabuwar nau’in cutar COVID-19

2021-11-28 16:39:50 CRI

Jiya Asabar kasar Kuwait ta sanar da janye sufurin jiragen sama na kai tsaye daga kasashen Afrika 9 sakamakon bullar sabon nau’in cutar numfashi ta COVID-19 mai suna Omicron.

Hukumar sadarwar kasar Kuwait ta ce, kasar ta dakatar da sufurin jiragen saman fasinja na kai tsaye daga kasashen Afrika ta Kudu, Namibia, Botswana, Zimbabwe, Mozambique, Lesotho, Eswatini, Zambia, da kuma Malawi, sai dai ban da manyan jiragen saman dakon kaya.

Kuwaiti ta kara da cewa, dukkan ‘yan kasar da suka fito daga kasashen tara za a killace su na tsawon kwanaki bakwai, inda dokar za ta fara aiki daga ranar 28 ga watan nan na Nuwamba, kuma za a bukace su yin gwajin cutar da zarar sun sauka a kasar, kana za su sake yin gwajin yayin da suka cika kwanaki shida da shiga kasar.

Haka zalika, wadanda ba ‘yan kasar Kuwait ba da suka fito daga wadancan kasashe tara, ko sun fito ne kai tsaye daga kasashen ko kuma sun bi ta wasu kasashen, ba za a ba su damar shiga kasar ba, sai dai idan sun zauna a wata kasar ta daban na tsawon kwanaki akalla 14.(Ahmad)

Ahmad