logo

HAUSA

Afrika CDC: Kasashen Afrika sun samu riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 400

2021-11-26 10:58:06 CMG

Afrika CDC: Kasashen Afrika sun samu riga-kafin COVID-19 sama da miliyan 400_fororder_211126-A1-cuta

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta bayyana cewa, wasu kasashen Afrika 54 sun samu alluran riga-kafin annobar COVID-19 kusan miliyan 403 ya zuwa yanzu.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana cikin alkaluman da take sabuntawa a duk mako cewa, kusan kashi 6.66 na al’ummar Afrika sun karbi cikakkun riga-kafin.

A cewar sanarwar, kimanin alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 221.7 daga cikin miliyan 403 da aka samar an riga an yi wa mutanen.

Kasashen Afrika biyar, da suka hada da Morocco, Masar, Afrika ta kudu, Algeria da Tunisia, su ne suka samu alluran riga-kafin COVID-19 mafi yawa, kuma sun baiwa al’ummun kasashen nasu, a cewar hukumar.(Ahmad)

Ahmad