logo

HAUSA

Kasar Sin ba za ta kawo tsaiko ga yarjejeniyar CTBT ba

2021-09-25 17:13:10 CRI

Kasar Sin ta nanata cewa, ba za ta taba zama tsaiko ga aiwatar da yarjejeniyar haramta gwajin nukiliya ta kasa da kasa ta CTBT ba.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana yayin taron kyautata hanyoyin fara aiwatar da yarjejeniyar cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka rattaba wa yarjejeniyar hannu, kasar Sin na girmama manufofi da kudurorinta. Kuma gwamnatin Sin ta dade tana kiyaye haramcin gwajin nukiliya.

Ya ce ana bukatar aiwatar da dangantaka ta hakika tsakanin kasa da kasa. Kuma ya kamata a warware sabani da rashin fahimta ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa, ta yadda za a samu yanayin siyasa mai kyau da yarjejeniyar za ta fara aiki.

Har ila yau, ya ce akwai bukatar adawa da ra’ayin cacar baka. Kuma dole ne a yi adawa da amfani da karfin soji, ta yadda za a samar da yanayin tsaro mafi dacewa na aiwatar da yarjejeniyar.

Bugu da kari, ya ce akwai bukatar adawa da yin gaban kai wajen janyewa daga yarjeniyoyi. Yana mai cewa ana matukar bukatar kiyaye mutunci da karfi da ingancin tsarin takaita makamai na duniya dake akwai, ta yadda za a samar da kwarin gwiwar fara aiki da wannan yarjejeniya. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha