logo

HAUSA

Iran ta dora alhakin harin da aka kai wa tasharta ta nukiliya kan Isra’ila

2021-07-07 10:32:09 CRI

Iran ta dora alhakin harin da aka kai wa tasharta ta nukiliya kan Isra’ila_fororder_伊朗

Gwamnatin Iran ta dora alhakin harin da aka kai wa tashar nukiliyarta dake kusa da birnin Karaj, a baya-bayan nan kan Isra’ila.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, Kakakin gwamnatin Iran Ali Rabiee, ya ce sun tabbatar da harin. Kuma ba a samu asarar rayuka ba, kana illar da aka yi wa kayayyaki ba ta da yawa.

Ya kara da cewa, rufin daya daga cikin rumfunan ya lalace, sai dai bai illata muhimman kayayyaki ba.

Ya ce Isra’ila ta yi hakan ne da zummar karkatar da tattaunawar nukiliyar kasar da ake yi, tare da aikewa da sakon cewa, duniya ba ta bukatar tattaunawa da Iran dangane da farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015.

A ranar 23 ga watan Yuni ne, kafofin watsa labaran Iran suka ruwaito cewa, an kai hari kan tashar nukiliyar kasar dake kusa da birnin Karaj, amma ba tare da bayanin asarar da ya haifar ba. (Fa’iza Mustapha)