logo

HAUSA

An gama wasan gwaji na farko na gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

2021-10-11 10:14:04 CRI

An gama wasan gwaji na farko na gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing_fororder_1011-01

An gama wasan gwaji na farko na gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, wato wasan gudun kankara cikin sauri ta kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, a jiya Lahadi. Yayin wasan, an dauki matakan kandagarkin cutar COVID-19, da kuma tabbatar da wasan bisa ma’aunin wasan gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu.

An shafe kwanaki uku ana yin wasan gudun kankara cikin sauri na kasar Sin a birnin Beijing, inda ‘yan wasa fiye da 20 daga kungiyoyin Sin da Koriya ta Kudu da kuma Netherlands suka halarci wasan. An tabbatar da gudanar da wasan bisa ma’aunin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu a dakin wasan gudun kankara cikin sauri na kasar Sin. (Zainab)