Sin za ta sayar da tikitin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ga ‘yan cikin kasar kawai
2021-10-11 15:12:20 CRI
Sin za ta sayar da tikitin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ga ‘yan cikin kasar kawai
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin ta yanke kudurin sayar da tikitin kallon gasar wasannin Olympics ta birnin Beijing ta lokacin hunturu dake tafe ne ga jama’ar dake cikin kasar kadai, saboda dalilai na kare rayukan al’umma.
Hua Chunying ta bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, inda ta amsa tambayar da wasu kafofin watsa labaran kasar Japan suka gabatar, game da gasar da za ta gudana a farko shekarar badi.
Jami’ar ta ce, an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa, an aiwatar da matakan kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19. Kuma an kai ga cimma matsayar hakan ne, bayan tuntuba tsakanin kwamitin shirya gasar na kasar Sin, da kwamitin shirya gasar Olympics na kasa da kasa.
Daga nan sai ta bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da cudanya da sauran kasashen duniya, wajen aiwatar da dokokin kasa da kasa yadda ya kamata, bisa salo na dimokaradiyya.
Za a fara wasannin gwaji na gasar wasannin Olymics na shekarar 2022 na Beijing a watan Oktoba
Masu shirya gasar wasannin Olympics da birnin Beijing zai karbi bakuncinta, sun sanar a yau Litinin cewa, za a shirya ayyukan gwaji kafin gasar wasannin Olympics ta Beijing da wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu na 2022, kuma ana iya barin ‘yan kallo su kalli wasu daga cikinsu.
Daga ranar 5 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba, za a shirya gasannin kasa da kasa guda 10, makonni uku na horo da gwaji guda biyu na cikin gida, don gwada dukkan wasannin a shiyyoyin gasar uku na Beijing, Yanqing da Zhangjiakou.
Bangarorin wasannin za su hada gudu kan kankara, kwarangwal, luge, gudun kankara na gajeren zango, tura mulmulen dutse na masu guragu, da tsaren keken amalanke, kwallon gora a kan kankara, wasan zamiyar falangen katako, da gudu da zamiya da takalmi a kan kankara da sauransu, kuma wasu za su kasance ga 'yan wasan cikin gida.
Kimanin 'yan wasa 2,000 daga kasashen waje, da jami'an kungiya, jami'an fasaha da ma'aikatan dake kula da lokaci da maki da ‘yan wasa suka samu ne ake sa ran za a gwada wadannan wasanni, kuma za su kasance karkashin kulawar jami’ai, tun lokacin da suka iso kasar Sin tare da ka'idojin dokoki na wurare daban-daban, a cewar masu shirya wasannin.