logo

HAUSA

Yakin Ciniki: Amurka Ta Ja Da Baya

2021-10-06 20:10:02 CMG

Yakin Ciniki: Amurka Ta Ja Da Baya_fororder_20211006-sharhi-yakin-ciniki-Bello

Katherine Tai, babbar jami’ar kasar Amurka mai kula da aikin ciniki, ta sanar da manufar gwamnatin shugaba Joe Biden dangane da kasar Sin a fannin cinikayya a ranar Litinin, inda ta ce kasar Amurka “ba ta son tsananta yanayi a fannin ciniki tsakaninta da kasar Sin”, kana tana shirin “kaddamar da muhawara tare da Sin da nuna gaskiya”. Idan an kwatanta da maganar Madam Tai, da barazanar da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kasar Sin ta ta da yakin ciniki, to, za a iya ganin cewa, kasar Amurka ta fara ja da baya.

Dalilin da ya sa haka, shi ne gazawar kasar Amurka a fannin dakile annobar COVID-19, wadda ta haifar da dimbin illoli ga tattalin arzikinta. Alkaluma sun nuna cewa, hauhawar farashin makamashi a kasar ta kai kashi 24.9% a watan Agustan bana kadai, kana matsakaiciyar hauhawar farashin kayayyaki a kasar ta kai kashi 4.3% a watan, wadda ta zama irinta mafiya yawa cikin shekaru 30 da suka wuce. Kana daya daga cikin dalilan da suka sanya ake samun wannan hauhawar farashi, shi ne yadda bazuwar annoba ta gurgunta wasu bangarorin masana’antu, da haddasa karancin ma’aikata.

Yanzu haka ana fama da matsalar rashin kayayyakin da ake bukata wajen hada abinci a dimbin wuraren sayar da abinci na kasar. Sa’an nan makarantu da yawa na kasar Amurka sun kasa samar da abinci masu inganci ga dalibai, sakamakon yadda suke fuskantar matsalar rashin abinci. Ban da wannan kuma, wani dalili na daban da ya sa ake samun hauhawar farashin kayayyaki, shi ne manufar kasar Amurka ta zuba makudan kudi cikin kasuwa don tabbatar da samun karuwar tattalin arziki.

Wannan manufa na tare da illolin samun hauhawar farashin kayayyaki, gami da yawancin bashi. Yanzu yawan bashin da ake bin gwamnatin kasar Amurka ya kusan kai dala triliyan 28.43, wanda ya zarce adadin da dokar kasar ta kayyade. Saboda haka, idan majalissun kasar sun kasa zartas da dokar daga adadin bashin da gwamnati za ta iya samu, ko kuma a dakatar da kayyadewar, kafin ranar 18 ga watan da muke ciki, to, gwamnatin kasar Amurka za ta fuskanci matsalar kasa biya bashi, a karon farko cikin tarihin kasar.

Karkashin wannan yanayi mai kunci a fannin tattalin arziki, kamfanoni da al’ummomin kasar Amurka, sun kasa ci gaba da jure wahalhalun da yakin ciniki ya haifar musu. An ce, tun bayan da kasar Amurka ta kaddamar da yakin ciniki da kasar Sin, jama’ar kasar Amurka sun biya karin kudi har fiye da dala biliyan 90, sakamakon karin harajin kwastam da gwamnatinsu ta karba.

Sa’an nan a watan Agustan bana, wasu manyan rukunonin ‘yan kasuwa 30 na kasar Amurka a hade sun rubuta wasika ga shugaba Biden na kasar, don neman a rage harajin da ake karba kan kayayyakin da aka samar a kasar Sin, inda suka ce manufar ta ba jama’a da kamfanonin kasar Amurka karin wahalhalu, da haddasa matsala ga tattalin arzikin kasar.

Ban da wannan kuma, wani dalili mafi muhimmanci da ya sa kasar Amurka ta fara ja da baya a yakin ciniki da ta kaddamar, shi ne Amurka ta ga yakin cinikin ya kasa yi wani tasiri kan tattalin arzikin kasar Sin. Ko da yake kasar Amurka tana karbar karin haraji kan kayayyakin da aka shigar da su daga kasar ta Sin, duk da haka, yawan kudin cinikin da aka yi tsakanin Sin da Amurka, daga watan Janairu zuwa na Agustan bana, ya karu da kashi 26%. Kana tattalin arzikin Sin na ci gaba da karuwa cikin sauri, bisa nagartattun matakan da kasar ta dauka ta fuskar hana yaduwar cutar COVID-19, da taimakawa kamfanoni tinkarar kalubale, da janyo hankalin masu zuba jari. Har ma bankin duniya ya bayyana a cikin wani rahoton da ya gabatar a karshen watan Satumba cewa, yana sa ran ganin karuwar tattalin arzikin Sin a shekarar 2021 zai kai kashi 8.5%, wanda zai zarce adadi na sauran kasashen dake shiyyar Asiya da tekun Pasifik, bisa hasashen da ya yi.

Yanzu kasar Amurka ta zama tamkar wani mutum da ya ta da rikici, wanda daga bisani ya ga babu damar samun nasara, don haka ya daina fada, ya fara ja da baya, sai dai za ta ci gaba da fadin wasu kalmomi marasa dadin ji don nuna cewa tana da karfi. A wannan karo, Madam Tai ta ce, kasar Amurka za ta hada gwiwa da wasu abokanta, don tsara wasu ka’idojin cinikin kasa da kasa “mai adalci”, da yin amfani da duk wani nau’in manufa don kare moriyar kasar. Amma a hakika, ta la’akari da wani mawuyacin hali da kasashe daban daban suke fuskanta a fannin tattalin arziki, a wannan lokaci da muke ciki, tana fama da annobar COVID-19, duk wata kasa za ta fi mai da hankali kan aikin karewa, da raya tattalin arzikin kanta. Wace ce daga cikinsu ke son taimakawa kasar Amurka, wadda ta fi nuna son kai da rashin daukar nauyi a duniya, wajen ta da rikici da kasar Sin?

Ban da haka, gwamnatin kasar Amurka ta riga ta dauki dimbin matakai don takara da kasar Sin, inda ta karbi karin haraji kan kayayyakin da ake samar a kasar Sin, da jefa takunkumi kan wasu manyan kamfanonin kasar Sin, da dai sauransu. Sai dai mene ne sakamakon da aka samu? Tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin sauri, yayin da cinikin da ake yi tsakanin kasashen Sin da Amurka shi ma sai karuwa yake yi.

Saboda haka, ya kamata kasar Amurka ta daidaita manufofin ta a fannin hulda da kasar Sin. Ta kara yin hadin gwiwa da Sin, maimakon ta da rikici. Kana ta kara musayar ra’ayi tare da Sin, maimakon matsawa kasar lamba. Ta wannan hanya, al’ummar kasar Amurka za su samu alfanu, yayin da tattalin arzikin kasashe daban daban shi ma zai samu karin damammakin farfadowa. (Bello Wang)

Bello