logo

HAUSA

Dawowar Meng Wanzhou Gida Kasar Sin Ta Nuna Yadda JKS Ke Mayar Da Jama’arta Gaban Kome

2021-09-25 21:03:00 CRI

Sakamakon kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi ba tare da tsayawa ba, ya sa a ranar 24 ga wata bisa agogon wurin, Meng Wanzhou, mataimakiyar shugaban kamfanin Huawei na kasar Sin ta shiga jirgin sama da kasar Sin ta yi shata ta kama hanyarta ta dawowa gida, bayan ta dauki kwanaki 1028 ana tsare da ita a kasar Canada ba bisa doka ba.

Meng Wanzhou ta sake samun ‘yanci ne saboda doka da adalci sun samu nasara, lamarin da ya nuna yadda JKS da ke mulkin kasar Sin da kuma gwamnatin Sin suke tsayawa kan kiyaye halaltattun hakkokin jama’arta, da kuma yadda jama’ar Sin ba sa jin tsoron siyasar fin karfi, suna kuma adawa da danniya.

A watan Disamban shekarar 2018, bisa bukatar gwamnatin Amurka, mahukuntan Canada suka tsare Meng Wanzhou a filin jirgin saman kasa da kasa na Vancouver, wadda ta yada zango a filin jirgin saman. Daga bisani Amurka ta bukaci a mika mata Meng Wanzhou don gurfanar da ita a gaban kotu bisa tuhumarta da laifin yin zamba ta hanyar aikawa da kudi ta na'urar lantarki ta telegraf. Canada ta yi biris da gaskiya ta tsare Meng Wanzhou ba bisa doka ba har kwanaki fiye da dubu 1, wato Meng Wanzhou ba ta saba dokokin Canada ba.

Kowa ya fahimci cewa, lalle Amurka da Canada ne suka yi wa Meng Wanzhou kazafi na siyasa. Da sunan doka suka danne kamfanonin kimiyya da fasahar zamani na kasar Sin, da zummar hana ci gaban kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha.

Bayan da aka tsare Meng Wanzhou ba bisa doka ba, gwamnatin Sin ta yi ta bukatar Canada da ta dakatar da goyon bayan Amurka, ta gyara kuskure nan take, ta ‘yantar da Meng Wanzhou, ta bar ta dawo gida. A watan Yulin bana, yayin da mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka Wendy Sherman take ziyara a kasar Sin, kasar Sin ta gabatar wa Amurka takardu guda 2, inda ta bukaci Amurka da ta soke umurnin mika mata Meng Wanzhou. A yayin taron majalisar kiyaye hakkin dan Adam na MDD karo na 48, kasar Sin ta nemi Canada ta soke umurnin tsare Meng Wanzhou.

Matakan da JKS da ke mulkin kasar Sin da gwamnatin kasar Sin suka dauka sun nuna yadda suke kokarin tafiyar da harkokin kasa domin moriyar jama’a, suna kuma sanya jama’a a gaban kome. A karkashin shugabancin JKS, har kullum kasar Sin tana mara wa jama’arta baya wajen daidaita matsaloli. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan