logo

HAUSA

Yankin raya masana’antun fasahohin zamani na Zhongguancun na kasar Sin ya samu karin kudin shiga

2021-10-03 16:12:09 CMG

Yankin raya masana’antun fasahohin zamani na Zhongguancun na kasar Sin ya samu karin kudin shiga_fororder_1003-ZhongGuangCun-Faeza

Katafaren yankin raya masana’antun fasahohin zamani na Zhongguancun, da ake wa lakabi da “Silicon Valley” na kasar Sin, ya samu karin kaso 27.8 kan kudin shigarasa a watanni 8 na farkon bana, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

A cewar hukumar kiddidiga ta birnin Beijing, kudin shigar da yankin mai manyan kamfanoni fasaha ya samu tsakanin watannin Junairu zuwa Augustan bana, ya kai yuan triliyan 5.2, kwatankwacin dala biliyan 807.

A cewar hukumar, kamfanonin bangarorin fasahar sadarwa da laturoni, da fannin injiniya mai nasaba da halittu da sabbin fasahohin kiwon lafiya, sun samu dorewar ci gaba.

Adadin ma’aikata a fannin bincike da kirkire-kirkiren fasaha a kamfanoni dake yankin Zhongguancun, ya kai 751,000 a wancan lokaci, adadin da ya karu da kaso 8.9 akan na makamancin lokacin a bara.

Zhongguancun da aka kafa a shekarar 1988 a arewa maso yammacin birnin Beijing, wanda ya kunshi jami’o’i da cibiyoyin bincike, shi ne yankin raya masana’atun fasahohin zamani na farko a kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)

Bello