logo

HAUSA

Beijing za ta inganta yanayin harsunan waje domin wasannin lokacin hunturu

2021-03-25 15:50:59 CRI

Ofishin kula da harkokin waje na gwamnatin birnin Beijing, ya ce an amince da wani shiri na musammam dake da nufin inganta yanayin harshen waje a birnin, domin wasannin lokacin hunturu.

Shirin ya shafi bangarori 5 da suke bukatar a inganta su, wadanda suka hada da fannonin amfani da harshen waje a Beijing yayin gasar Olympic ta lokacin hunturu, da inganta alamomi dake cikin harshen wajen da karfin samar da hidimomi cikin harshen waje a birnin da halatta amfanin da harshen da kuma damawa da al’umma cikin shirin da nufin inganta yanayin amfani da harshen waje ta kowanne bangare. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha