logo

HAUSA

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Dawowar Meng Wanzhou

2021-09-25 20:23:06 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce matsayar kasar Sin kan shari’ar Meng Wanzhou a bayyane take kuma ba ta taba sauyawa ba.

Hua Chunying ta ce, shaidu sun nuna cewa batu ne na zalunci kan ‘yar kasar Sin da nufin danne kamfanonin fasaha na kasar.

Ta ce, laifukan da ake ikirarin ana tuhumar Meng da aikatawa na bogi ne, tana mai cewa, bankin HSBC da Amurka ke cewa shi aka damfara, ya fitar da bayanan da suka wanke Meng.

A cewarta, Amurka da Canada sun tsare ta ne kawai ba tare da wata shaidar dake tabbatar da ta aikata laifi ba. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha