logo

HAUSA

Wadanne alfanu shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta kawo wa nahiyar Afirka?

2021-09-07 20:22:05 CMG

Wadanne alfanu shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta kawo wa nahiyar Afirka?_fororder_20210907-sharhi-B&R-Bello

Shekaru 8 da suka wuce, wato a ranar 7 ga watan Satumban shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar gina “Zirin tattalin arziki na hanyar siliki”. Daga bisani, ya kara ba da wata shawarar da ake kira “hanyar siliki dake kan teku ta karni na 21”. Wadannan shawarwari 2 da suke hade sun zama shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da wannan shawara ce da nufin karfafa huldar hadin kai tare da sauran kasashe, don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin dan Adam.

Alkaluma sun nuna cewa, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta shafi hakikanin matakai: Daga shekarar 2013 zuwa 2020, kasar Sin ta kulla kwantiragi tare da kasashe masu alaka da shawarar da darajarsu ta zarce dalar Amurka biliyan 940. Kana yawan jarin da kasar Sin ta zuba wa wadannan kasashe kai tsaye, ya kai dalar Amurka biliyan 136.

Ba shakka kasashen Afirka su ma sun nuna sha’awa sosai ga shawarar. Zuwa yanzu akwai kasashe 46 dake nahiyar Afirka da suka kulla yarjeniyoyi masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” tare da kasar Sin, wadanda suka fara ganin alamar samun ci gaba cikin sauri: Zuwa watan Yunin bana, kamfanonin kasar Sin sun kafa yankunan masana’antu 45 a kasashe a kalla 16 dake nahiyar Afirka. Kana Sin tana gina manyan ayyukan samar da wutar lantarki 56 a kasashe a kalla 23 dake Afirka. Ban da wannan kuma, kasar Sin tana gina layin dogon da tsawonsa ya kai kilomita 17309, da tashohin jiragen ruwa 33, a kasashe a kalla 17 na Afirka.

Jama’ar kasashe daban daban sun fi jin dadin kayayyakin more rayuwa da aka gina. A Mauritus dake gabashin Afirka, wani kamfanin kasar Sin ya gina wata madatsar ruwa a dab da birnin Port Louis na kasar, wadda ta kawo karshen matsalar karancin ruwa da birnin ke fuskanta, ta yadda mazauna wurin suke iya samun famfo. A kasar Kenya kuma, layin dogon da aka gina a tsakanin Mombasa da Nairobi, ya rage lokacin zirga-zirga a tsakanin biranen daga sa’o’i 10 zuwa sa’o’i 4. Ya kuma sanya ‘yan kasuwan kasar murna sosai, domin kudin da suke kashewa wajen jigilar kaya ya ragu da kashi 79%.

Duk wadannan manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, an fara samun moriya daga gare su ne, tun lokacin da aka fara gina su. A Najeriya, matasa sun samu dimbin guraben aikin yi, yayin da ake aiwatar da ayyukan gina layin dogo na Abuja-Kano, da na Lagos-Ibadan, da layin jirgin kasa a birnin Abuja, da sauran su. A kamfanin dake aikin zirga-zirgar jirgin kasa na birnin Abuja kadai, an dauki ma’aikata da yawansu ka iya kai fiye da dubu 1. Kana a ma’aikatar hada tarago da wani kamfanin kasar Sin ke ginawa a Najeriya, an ce za a samu guraben aikin yi 5000.

Ci gaban aikin gina kayayyakin more rayuwa ya sa ana bukatar karin kwararrun ma’aikata. Saboda haka hadin gwiwa a fannin aikin ilimi shi ma ya zama wani muhimmin bangare na shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, ta hanyar gudanar da kwas na gajeren lokaci, kasar Sin ta taimaki kasashen Afirka wajen horar da mutane fiye da dubu 300, wadanda suka zama kwararru a fannonin aikin gona, da kula da itatuwa, da kare muhalli, da dai sauransu. Kana kasar Sin ta kafa kwalejin Lu Ban mai ba da damar karatun digiri, da horaswa, guda 10 a kasashen Afirka, inda ake koyar da ilimi a wasu bangarori 23, da suka hada da sabbin makamashi, da kula da jirgin kasa, da hada injuna, da dai sauransu.

Wani abun da ya fi janyo hankalin mutane game da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” shi ne yadda take tabbatar da moriyar bangarori daban daban, wannan ya sa shawarar ta zama mai dorewa. Ta hanyar wannan shawara, kasar Sin za ta iya sabunta tsare-tsaren masana’antu a gida. Yayin da a nasu bangare, kasashen Afirka za su samu damar raya kayayyakin more rayuwa, bisa taimakon da kasar Sin ta ba su, gami da karbar wasu bangarorin masana’antu na kasar Sin, ta yadda su ma za su iya raya masana’antunsu na cikin gida, da habaka bangaren fitar da kayayyaki zuwa ketare, daidai kamar yadda kasar Sin ta samu damar raya masana’antu a baya. Daga baya, sannu a hankali za su kama hanyar samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri.

Kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suna kallon kasar Sin a matsayin abokiyar takara, saboda haka su kan yi amfani da tunaninsu na yakin cacar baki da na tsoffin ‘yan mulkin mallaka wajen shafawa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” kashin kaza, lamarin da ya yi tasiri kan wasu kasashen Afirka game da yadda suke kallon shawarar. Dangane da wannan batu, na kan tuna da maganar Seyoum Mesfin, tsohon ministan harkokin wajen kasar Habasha, wanda ya ce “ Yayin da ake yanke shawara, ya kamata kasashen Afirka su lura da abubuwan da ya kamata a ba su fifiko. Inganta kayayyakin more rayuwa, da neman samun ci gaba cikin sauri, da rage talauci suna da matukar muhimmanci ga nahiyar Afirka, kana su ne muhimman fannonin da Sin da Afirka suke hadin gwiwa a kai. “ Ci gaban tattalin arziki yana da muhimmanci sosai. Illa dai ana samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, to, ba wata matsala da ba za a iya daidaita ta ba. Wannan wata muhimmiyar fasaha ce ta kasar Sin, wadda ta kasance dalilin da ya sa dimbin kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen dake nahiyar Afirka da yawa, ke karbar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da hannu biyu-biyu. (Bello Wang)

Bello