logo

HAUSA

Ya kamata kasashen yamma su daidaita ra’ayinsu game da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya

2021-09-16 20:34:23 CMG

Ya kamata kasashen yamma su daidaita ra’ayinsu game da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya_fororder_20210916-sharhi-BRI-Bello

A kwanan baya, na rubuta wani bayani don bayyana alfanun shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kasar Sin ta gabatar ga kasashen Afirka. Sa’an nan don neman samun daidaito a tsakanin ra’ayoyi daban daban, a yau bari mu duba ra’ayoyin kasashen yammacin duniya dangane da shawarar, kana mu yi bincike ko ra’ayoyinsu na da ma’ana.

Da zarar an ambaci huldar dake tsakanin Sin da Afirka, kasashen yamma su kan nuna wani ra’ayi na hassada. A ganin su tun da sun kasa samar da dimbin tasiri kan kasashen Afirka yanzu, ba sa son ganin wata kasa ta daban ta samar da karin tasiri a nahiyar Afirka. Kana abun da ya fi ban sha’awa shi ne, al’ummun kasashen yamma suna son daukar wasu munanan ayyukan da suka taba aikatawa a kasashen Afirka, sa’an nan su dora su a kan kasar Sin. Misali tsohon minista mai kula da harkokin waje na kasar Birtaniya, Jack Straw, ya taba bayyana cewa, “ayyukan da kasar Sin take yi a Afirka sun yi kama da abubuwan da kasar Birtaniya ta yi wasu shekaru 150 da suka wuce.” A nata bangare, Hilary Clinton, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka, ita ma ta taba bayyana cewa, wai kasar Sin na “fakewa da batun zuba jari”, tana neman “yin mulkin mallaka” a kasashen Afirka.

Hakika shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ko (BRI), ta shafi wasu kasashe fiye da 60 da suka kasance a dab da Zirin da Hanyar, kana fiye da rabinsu suna nahiyar Afirka. Don haka kasar Sin a karkashin shawarar BRI, ta zuba dimbin kudi a nahiyar Afirka don gina sabbin kayayyakin more rayuwa a can. Wannan zuba jari yana tattare da burin samun riba. Amma yadda kasashen yamma suke siffanta shawarar BRI tamkar jirkita hujjoji ne, kasancewar bayanansu ba sa bayyana gaskiyar huldar dake tsakanin Sin da Afirka.

Shahararren mai nazarin tarihi Walter Rodney, ya taba rabutawa a cikin littafinsa mai taken “Yadda kasashen Turai suke haddasa koma bayan tattalin arziki a Afirka”, cewa a karkashin tsarin mulkin mallaka da kasashen yamma suka yi, “kasashen Afirka ba su samu komai ba, illa dai dogaro kan kasashen yamma, da dadadden koma bayan tattalin arziki”. A akasin haka kuwa, kasar Sin na kokarin nisanta kanta da tunanin ‘yan mulkin mallaka na kasashen yamma, wadanda ke son ci da gumin sauran kasashe, da tsoma baki cikin harkokinsu na gida, daga dukkan fannonin siyasa da tattalin arziki. A karkashin manufar tabbatar da samun ribar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, kasar Sin ta mai da karin hankali kan abubuwan da kasashen Afirka suke bukata, wato wasu manyan kayayyakin more rayuwa, wadanda za su zama tushen samun ci gaban tattalin arziki.

A karkashin tsarin shawarar BRI, kasar Sin ta riga ta halarci wasu manyan ayyukan more rayuwar jama’a fiye da 200 na kasashen Afirka, ta hanyar tattara kudi, da daukar nauyin aikin gini. Sa’an nan ayyukan da kamfanonin kasar Sin suka kammala a nahiyar Afirka, da wadanda suke ginawa, sun hada da ginawa da sabunta hanyoyin mota na tsawon kilomita dubu 30, da layin dogo na kilomita dubu 2. Kana a bisa taimakon da kasar Sin ta bayar, nahiyar Afirka na samun karin tashohin jiragen ruwa (wadanda ke daukar karin kayayyaki har ton miliyan 85 a kowace shekara), da karin ma’aikatun tace ruwa (wadanda ke samar da karin ruwa mai tsabta fiye da ton miliyan 9 a kowace rana), da karin na’urorin samar da lantarki (masu samar da karin wutar lantarki har megawatt dubu 20 a kowace shekara), gami da sabbin layukan lantarki na fiye da kilomita dubu 30 a kowace shekara.

A cewar Ehizuelen Michael M.O., wani shehun malami dan Najeriya, dake aiki a cibiyar nazarin Afirka a jami’ar koyar da ilimin malanta ta Zhejiang dake kasar Sin, yadda kasar Sin take taimakawa kasashen Afirka gina kayayyakin more rayuwa yana da ma’ana sosai, domin ta wadannan kayayyaki, kasashen Afirka za su samu damar raya masana’antu na kansu, da kawo karshen dogaro kan kasashen yammacin duniya da sauran kasashen ketare.

Matsalar da take damun kasashen yamma ita ce, ba su fahimci wajibcin ciyar da tattalin arzikin kasashen Afirka gaba, ta hanyar zuba jari da hadin gwiwa ba, kana ba su san za a iya samun riba, ta hanyar taimakawa kasashen Afirka inganta kayayyakin more rayuwa ba. Saboda haka suna waswasin ko su zuba karin jari a Afirka ko a’a. A nata bangare, kasar Sin ta gudanar da ayyukan da su kasashen yamma ba su taba yi ba, tare da taimakawa kasashen Afirka samun hakikanin ci gaba. Wannan shi ne dalilin da ya sa kasashen Afirka ke zama kut da kut da kasar Sin, duk da cewa su kan ji yadda ake yada jita-jita dangane da Sin da shawararta ta BRI.

Idan da gaske ne ana son tabbatar da moriyar kasashen Afirka, me ya sa za su shafa kashin kaji kan matakan da za su taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba? Hakika a nata bangare, kasar Sin ba ta taba bayyana wani abu maras kyau game da zuba jari da ba da tallafi da kasashen yamma suka taba yi a kasashen Afirka ba, kana kasar Sin har kullum tana neman hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin taimakawa Afirka samun ci gaba. Idan ana son tabbatar da moriyar dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, to, ya kamata kasashen yammacin duinya su daina dora wa kasar Sin laifi, da amincewa da gudunmowar da kasar Sin ta samar a fannin raya kasashen Afirka, gami da yarda da matsayin shawarar BRI, na wani muhimmin dandalin gudanar da hadin gwiwar kasa da kasa, don neman taimakawa kasashen Afirka samun ci gaba. (Bello Wang)

Bello