logo

HAUSA

Har yanzu nahiyar Afirka na fuskantar kalubale a fannin yaduwar annobar COVID-19

2021-09-12 17:35:30 cri

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka, a ranar 11 ga wata ta bayyana cewa, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afirka ya zarce miliyan 8. A halin yanzu, yanayin tinkarar annobar da nahiyar Afirka ke ciki na samun kyautatuwa, kuma ana gudanar da aikin samar da allurar rigakafi da yin allurar rigakafi yadda ya kamata. A waje guda kuma, har yanzu Afirka na fuskantar kalubale ta fuskokin sauyin nau’ikan cutar da karancin yin alluran riga kafin da dai sauransu.

A ranar 9 ga wata, ofishin hukumar WHO a Afirka ya ce, yanzu yanayin yaduwar annobar karo na uku a nahiyar na samun kyautatuwa.

Ko da yake, an samu sassauci kan yanayin annobar a Afirka, kuma ana ta inganta aikin yin allurar riga kafin, amma har yanzu ana fuskantar kalubale a fannoni masu yawa. Daraktar ofishin, Matshidiso Rebecca Moeti ta ce, sakamakon tasirin cutar nau’in Delta mai saurin kamuwa ke yi, idan an kwatanta da yanayin yaduwar annobar na da, yanayin na yanzu yana raguwa sannu a hankali.

Bisa kididdigar da cibiyar kula da cututtuka ta Afirka ta bayar an nuna cewa, a halin yanzu, jimillar alluran riga kafi da aka yi a nahiyar Afirka ta kai miliyan 111.3, kuma an yiwa al’ummar nahiyar riga kafin kusan kashi 3.18%, adadin da yayi kasa a bisa makamancin sauran sassan duniya.

Moeti ta ce, yayin da Afirka ke yin bakin kokarin ta na daukar matakan kiwon lafiyar jama'a, a waje guda kuma dole ne ta karfafa karfinta na samar da alluran riga kafi da kuma yin alluran riga kafin, hakan za a iya kyautata yanayin yaduwar annobar. (Bilkisu)