logo

HAUSA

Jakadan Sin: Ayyukan Hukumar UNHCR Na Fuskantar Gagarumin Kalubale

2021-09-25 16:53:32 CRI

Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Chen Xu, ya ce ayyukan hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD na fuskantar gagagrumin kalubale a yanzu.

Da yake jawabi a madadin kasashen da suke da ra’ayi iri guda game da inganta daidaito da adalci a bangaren kare hakkin dan Adam, yayin taron majalisar kula da hakkin dan Adam karo na 48, Chen Xu, ya ce ka’idojin tabbatar daidaito da kaucewa bangaranci da wariya, na cikin hadari.

Ya ce wasu kasashe, wadanda ke yin biris da matsalolinsu na hakkin dan Adam saboda manufofin siyasa, na ci gaba da katsalandan cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam, a yunkurinsu na kakaba tsarukansu a kan wasu.

Jami’in na kasar Sin ya bayyana cewa, hakan tamkar raina cikakken iko da ‘yancin kasashe ne da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, kana yana illata kokarin da duniya ke yi na ingantawa tare da kare hakkokin bil Adama.

Ya ce kamata ya yi, kasa da kasa su hada hannu wajen adawa da irin wannan dabi’a. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha