logo

HAUSA

Kasar Sin za ta yi takarar zama memba a majalisar harkokin hakkin dan Adam ta MDD

2021-09-14 20:17:46 cri

Yau Talata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya kira taron manema labarai, don yin takaitaccen bayani kan muhimman abubuwan dake cikin Shirin Ayyukan Kare Hakkin Dan Adam na Kasa (2021-2025).

Wakiliyar musamman ta ma’aikatar harkokin wajen kasar mai kula da harkokin hakkin dan Adam, madam Li Xiaomei ta bayyana cewa, kasar Sin za ta shiga aikin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa ta fannoni hudu.

Da farko, za ta sauke nauyin dake wuyanta a duniya a fannin kare hakkin dan Adam cikin tsanaki. Na biyu, za ta shiga ayyukan hukumar harkokin hakkin dan Adam ta MDD sosai, inda za ta yi takarar zama mamba ta majalisar harkokin hakkin dan Adam ta MDD a tsakanin shekaru 2024 zuwa 2026. Na uku, za ta gudanar da tattaunawa da hadin kai, game da batun hakkin dan Adam. Na hudu, za ta shiga ayyukan gudanar da harkokin hakkin dan Adam sosai. (Mai fassara: Bilkisu Xin)