logo

HAUSA

Wakilin Sin: Doka Da Odar Kasa Da Kasa Cikin Adalci Da Demokuradiya Na Da Muhimmanci Wajen Kare Hakkin Bil-Adama

2021-09-21 15:51:03 CRI

Shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya fadawa hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD cewa, doka da odar kasa da kasa cikin adalci da demokuradiya na da muhimmanci wajen ingantawa da ma kare hakkin bil-Adama.

Da yake jawabi a madadin wasu kasashe, yayin tattaunawar mu’amala da kwararre mai zaman kansa na MDD kan inganta doka da odar kasa da kasa cikin adalci da demokuradiya, Chen Xu ya jaddada muhimmancin tsarin kasashen duniya karkashin jagorancin MDD, da doka da odar kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa, yana kuma adawa da cin zarafi da ra’ayi na kashin kai, da nuna fuska biyu.

Jakadan na Sin ya kuma yi kira ga dukkan kasashe, da su ci gaba da yin hadin gwiwa da samun nasara tare, da gudanar da tattaunawa da hadin gwiwa bisa tushen daidaito da mutunta juna, da warware bambance-bambance ta hanyar tuntuba da tattaunawa. Ya kuma bukaci bangarori, da su kasance masu bude kofa da tafiya da kowa, da mutunta bambancin wayewar kai da hanyoyin ci gaba da kasashe suka zaba da kansu, da kaucewa tilasta tsarin zamantakewar wata kasa kan wata ta daban ko haddasa rarrabuwa da yin fito na fito.

Ya kuma lura da cewa, a fagen kare hakkin dan Adam, ya kamata dukkan bangarori su kiyaye ka’idoji na dunkuliya, da rashin nuna son kai, adalci, da rashin nuna zabi da kaucewa siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam ko tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe.(Ibrahim)

Ibrahim