logo

HAUSA

Wakilin Sin: Tilas ne a bincika muggan laifukan da Amurka ta aikata a Afghanistan

2021-09-15 11:14:33 CMG

Wakilin Sin: Tilas ne a bincika muggan laifukan da Amurka ta aikata a Afghanistan_fororder_210915-A2-Amurka

Jiang Duan, ministan ofishin jakadancin kasar Sin a MDD dake Geneva, ya bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa a rana ta biyu na taron kolin hukumar kare hakkin dan adam ta MDD karo na 48 cewa, a madadin gamayyar kasashen, yakin da Amurka ta jagoranta ya haifar da mummunar hasarar rayuka gami da raba fararen hula da muhallansu.

Sanarwar ta kuma bayyana damuwa game da dadaddun batutuwan dake shafar hakkin dan adam da ake zargin Amurka da aikatawa inda aka bukaci hukumar kare hakkin dan adam ta MDD da babban kwamishinan hukumar kare hakkin dan adam, da su ci gaba da bibiyar yanayin hakkin dan adam a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, a maimakon Amurka ta ba da cikakkiyar himma wajen yaki da annobar COVID-19, sai dai gwamnatin Amurkar tafi mayar da hankali kan batutuwan batanci irin na siyasa kamar batutuwa irin su binciken asalin kwayar cutar, da nufin dora zargi kan sauran kasashe, da kuma yin watsi da nauyin dake bisa wuyanta saboda gazawarta.

A cewar sanarwar, halayyar nuna wariyar launin fata da nuna banbanci da kyama sun jima da samun gindin zama a Amurka. ‘Yan Afrika da mutanen dake da tushe na Afrika, da ‘yan Asiya da mutanen dake da tushen Asiya, da musulmi da sauran tsirarun ‘yan kananan kabilu suna ci gaba da fuskantar muzgunawa da cin zarafi a kasar.(Ahmad)

Ahmad