logo

HAUSA

Tawagar MDD ta gana da sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea

2021-09-14 11:11:52 CMG

Tawagar MDD ta gana da sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea_fororder_fa'iza-3

Manzon musammam na MDD a yankin yammacin Afrika da Sahel, Mahamat Saleh Annadif, ya gana da shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea, Mamadi Doumbouya da shugaba Alpha Conde dake tsare.

A cewar Mahamat Annadif, manufar ziyarar tasa ita ce, ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki, da zummar fahimtar bukatunsu da yadda MDD da sauran hukumomin kasa da kasa za su taimakawa kasar tabbatar da zaman lafiyar da kwanciyar hankali da kuma hadin kai.

Har ila yau a jiyan, tawagar da ta MDD ta gana da Mamadi Doumbouya da Alpha Conde, da wakilan bangaren adawa na kasar da jakadun kasashe daban-daban dake kasar, da kuma wakilan al’umma. A cewar Mahamat Annadif, MDD za ta ci gaba da tuntubar Tarayyar Afrika da kungiyar ECOWAS dangane da yanayi na Guinea, yana mai cewa, kaucewa da rikici, ya dogara ne kan al’ummar kasar. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza