logo

HAUSA

Sin: Australiya tana yunkurin dauke hankalin jama’a ne kawai

2020-12-01 20:34:17 CRI

Dangane da zargin wai “hoton jabu” da kasar Australiya ta yi kan zanen da Zhao Lijian, kakaki daban na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya wallafa a shafinsa na Twitter game da al’amarin hallakar fararen hula da sojojin Australiya suka yi a kasar Afghanistan, madam Hua Chunying, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Talata cewa, ainihin nufin Australiya na yin wannan zargi shi ne, domin dauke hankalin duniya da kuma matsawa kasar Sin lamba, wadda a baya aka matsa mata. Kasar Australiya tana son kwace ikon kasar Sin na bayyana hakikanan abubuwan da suka faru.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Hua Chunying ta yi nuni da cewa, zanen da Zhao Lijian ya wallafa, zane ne da aka yi a kwamfuta, ba hoto ba ne. Madam Hua ta kuma nuna wasu hotunan da aka dauka kan yadda sojojin Australiya suka aikata ta’asa da kuma rahoton da ma’aikatar tsaron Australiya ta gabatar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan