Shin Scott Morrison Da Irinsa Suna Sokar Kasar Sin Ne Don Samun Kudi Daga Kasar Ta Sin?
2020-12-04 20:37:21 CRI
In an ambato ’yan siyasan kasa da kasa da suke saurin canza ra’ayi, ba za a taba mantawa da firaministan kasar Australiya Scott Morrison. Kwanan baya, ya bukaci kasar Sin ta nemi gafara daga wajen kasarsa dangane da wani zanen da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya wallafa a shafinsa na Tiwitter game da yadda sojojin Australiya suka aikata ta’asa a kasar Afghanistan. Amma jiya Alhamis ya sauya ra’ayinsa ba zato ba tsammani, inda ya yi shelar cewa, yana fatan tuntubar kasar Sin ta hanyar da ta dace. A cewarsa, huldar da ke tsakanin Australiya da Sin suna kawo moriyar juna tsakanin kasashen 2.
Yayin da ya shafa wa kasar Sin kashin kaji, mista Morrison yana kuma yunkurin neman samun kudi ne daga kasar Sin. Ko ya haukace ne? A cikin shekaru 2 ko fiye da haka da suka wuce bayan da ya zama firaministan Australiya, ya bi sahun kasar Amurka ta fuskar siyasa, inda ya rika sukar kasar Sin. Amma yana kokarin cin gajiyar bunkasuwar kasar Sin ta fuskar tattalin arziki. Sanin kowa ne cewa, mista Morrison ya yi dabara domin samun moriyar siyasa. Dalilin da ya sa haka shi ne domin wannan dan siyasa mai taurin kai kuma mai tunanin yakin cacar baki yana kallon kasar Sin bisa tunaninsa, yana kuma kokarin faranta ran Amurka, a yunkurin samun moriyar siyasa.
Idan mista Morrison yana son ya samu kasarsa da kasar Sin su amfana, to, ya kamata ya nuna sahihanci tukuna. Dole ne ya fahimci cewa, kasarsa ta Australiya ba ta da muhimmanci ko kadan yayin da wasu kasashen yammacin duniya suke yunkurin dakatar da ci gaban kasar Sin. Za kuma ta dandana kudarta idan ya bi umurnin wasu a nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific. Jama’ar Sin ba za su yarda da yadda wasu suke cin gajiyar ci gaban kasarsu, tare da yunkurin dakatar da bunkasuwar kasar Sin ba. Mista Morrison da sauran irinsa, ba za su taba cimma burinsu ba! (Tasallah Yuan)