logo

HAUSA

Firaministan Australiya Ya Sa Kasarsa Ta Zama Abin Dariya

2020-12-02 20:30:08 CRI

Firaministan Australiya Ya Sa Kasarsa Ta Zama Abin Dariya

Kwanan baya, wani rahoton da ma’aikatar tsaron kasar Australiya ta fitar ya yi cikakken bayani kan yadda sojojin kasar suka aikata ta’asa, inda suka kashe fararen hula bayin Allah a kasar Afghanistan, ciki had da yadda suka yiwa wasu ’yan shekaru 14 maza guda 2 yanka rago, suka kuma jefa gawawwakinsu cikin kogi. Kasashen duniya sun yi tir da abubuwan da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan.

Duk da irin ta’asar da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan, firaministan kasar Scott Morrison bai nemi gafara daga wajen al’ummar Afghanistan ba, a maimakon haka, ya nuna rashin jin dadi da wani zanen da wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya wallafa a shafin Twitter, wanda ya yi tir da ta’asar sojojin Australiya. Mista Morrison ya bukaci kasar Sin ta nemi gafara daga wajen kasarsa. Ko da yake daga baya mista Morrison ya ce, to, shi ke nan, a sa aya a wannan lamarin, saboda an bukaci a gurfanar da wadanda suka kashe mutanen farar hula a Afghanistan a gaban kotu. Amma abin da ya yi ya nuna mana cewa, wasu wadanda suke kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam, suna nuna fuska 2 kan batun kare hakkin dan Adam. Suna yunkurin dauke hankalin jama’a, ba su so a bayyana hakikanin abubuwan da suka faru.

Idan shugabannin Australiya ba su kara kyautata halayyar sojojin kasar ba, ba su kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifi a gaban kotu ba, sannan ba su nemi gafara daga wajen jama’ar Afghanistan ba, sun ci gaba da damun kasar Sin bisa wasu hujjoji maras dalili, to, za su zubar da kimar kasar ta Australiya, da ma kasashen yammacin duniya gaba daya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan